Na Gagara Magana Da Buhari Har Yanzu – Babajide

Gwamnan jihar Lagos Babajide Sanwo-Olu, ya ce har yanzu bai samu yin magana da shugaban kasa Muhammadu Buhari ba, kan hargitsin da aka samu a Lekki Toll Gate, ranar Talata.

A wata zantawa da aka yi da shi gidan talabijin na Arise TV a ranar Alhamis, Gwamnan ya ce sau biyu yana kokarin son yin magana da shugaban kasar amma bai yi nasara ba.

Ya ce a karo na farko da ya kira ofishin shugaban kasar, an sanar da shi bai shigo ofishin ba, da ya sake kira na biyu kuma aka ce masa ya riga ya shiga taron majalisar zartaswa.

Saidai kuma Sanwo-Olu, ya ce daga bisani Babban Hafsan Tsaron Nijeriya ya kira shi a ranar Larabar a bisa umarnin shugaban kasar, kuma ya tambaye shi idan yana bukatar a jibge masa dakarun sojoji a jihar.

Amma kuma gwamnan bai bayyana cewa ya amince da tayin ba ko a’a.

Ku kasance da shafin mu na www.muryaryanci.com domin Samun ingantattun labarai a fadin kasar nan da dumi dumin su

Related posts

Leave a Comment