Jawabin Shugaban Kasa: Buhari Ya Haramta Dukkanin Wata Zanga-Zanga A Najeriya

Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya dakatar da duk wani nau’in zanga-zanga a fadin tarayyar Najeriya, ba tare da wani ?ata lokaci ba.

A jawabin da shugaban yayi a daren Alhamis, ya ce ya dakatar da zanga-zanga ne saboda yadda rajin masu zanga-zangar #EndSARS ya canza zani a fadin tarayyar ?asar nan, inda ‘yan banin na iya masu ?oyayyiyar manuf suka kwace abin.

Shugaban kasan yace: “Saboda haka ina kira ga matasanmu su daina zanga-zanga kuma su shiga tattaunawa da gwamnati wajen neman mafita.”

“Ya zama wajibi a gare in muku jawabi akan halin da kasar nan ke ciki bayan tattaro bayanan da nayi musamman bayan ganawa da shugabannin tsaron kasar nan”.
Abin takaici ne yadda matasan mu suke neman sauyawa daga zanga zangar lumana zuwa wani abu na tashin hankali.
Dokar kasa ta ba kowane ?an kasa damar yin zanga zangar lumana musamman idan akayi la’akari da sashi na 40 cikin kundin tsarin mulkin kasar nan”.

“Amma kuma yana da kyau masu zanga zangar su sani cewa akwai sauran hakkin sauran ‘yan Najeriya da dokokin kasa”.

“Mun saurare koken ‘yan Najeriya musamman akan korafin da suka gabatar akan jami’an SARS. Kuma munyi alkawarin sauya tsarin aikin ‘yan sanda kamar yadda ‘yan kasa suka bukata. Sannan munyi alkawarin zamu saurare koken masu zanga zanga guda biyar dasu ka gabatar”.

“Amma abin takaici ne yadda wasu matasan ke fakewa da zanga zangar nan wurin aikata manyan laifuffuka kamar cin zarafin mutane, lalata fadar sarkin Legas, lalata filin tashin da sauka na jiragen sama, ?alle gidajen Yari, da kuma lalata kayayyakin Gwamnati”.

“Matasan basu tsaya anan ba, sun je kafar sada zumunta na zamani suna gayawa duniya ?arairayi kala kala wurin bata sunar ?asar su a idanun duniya”.

“Gwamnatin mu tana iya bakin kokarin ta wurin tallafawa rayuwar matasan kasar nan duk da kalubalen tattalin arziki da duniya ke ciki sakamakon bullar cutar covid 19.
Ba a taba samun Gwamnatin da ta bunkasa rayuwar matasan kasar nan kamar Gwamnatin mu ba, domin mun kawo shirye shirye da dama wa?anda suka ha?a….

A – Biyan albashin wata uku ga ma’aikatan kananan masana’antu dubu 100 a fadin kasar nan

B – Biyan kudaden rajistan kananan masana’antu 250,000

C – Ku?in Tallafin kasuwanci da bun?asa ?ananan sana’o’i da inganta fannin noma.

” ina kara kira ga ‘Yan Najeriya akan su kwantar da hankalin su domin a matsayin mu na masu koyi da mulkin dimokaradiyya, zamu tabbatar da yiwa kowa adalci akan tsare tsaren da zamu bullo dasu”

Related posts

Leave a Comment