Na Cika Alkawarin Da Na Yi Na Samar Da Tsaro Da Yakar Rashawa – Buhari

Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatin sa ta samu ci gaba sosai a kan alkawuran da ta ?auka na magance matsalolin tsaro da cin-hanci, inda ya ce ta kuma bun?asa tattalin arziki.

Buhari ya bayyana hakan ne a bikin yaye ?aliban kwalejin horon ‘?an sanda da ke Wudil a Jihar Kano ranar Alhamis.

A cewar Buhari, tuni gwamnatinsa ta ci ?arfin Boko Haram, IPOB, ESN da kuma ‘yan fashin daji, inda ya ?ara da cewa gwamnatin na ?ara ?o?arin magance matsalolin tsaron.

Shugaban ya ?ara da cewa gwamnatin sa ta magance cin hanci, inda ya ce ya yi ?o?ari sosai domin ganin ?asar bata koma lokacin gwamnatocin baya ba kan matsalar cin-hanci da rashawa.

Buhari ya ?ara da cewa tuni al’ummomin da Boko Haram da fashin daji ya yi wa barna sun fara koma wa ?auyuka da garuruwan su.

A nashi jawabin, Shugaban kwalejin, AIG Abdurrahman Ahmad ya yaba wa gwamnatin tarayya da sauran masu ruwa da tsaki bisa taimako da tallafin da su ke yi ga makarantar.

Sai dai kuma shugaban makarantar ya ce kwalejin na fuskantar tarin matsaloli da sai gwamnati ta shigo domin magance su.

Related posts

Leave a Comment