Rikicin Kabilanci: Rundunar ‘Yan Sandan Adamawa Ta Cafke Mutum Shida

A kokarin ta na maido da zaman lafiya biyo bayan rikicin kabilanci da aka yi a kananan hukumomin Lamurde da Guyuk a jihar Adamawa, yanzu haka rundunan lyan sandan jihar tana tsare da mutane shida wadanda ake zargi da hannu a rikicin.

Kakakin rundunan ‘Yan sandan jihar SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar kuma aka rabawa manema labarai a Yola.

SP Suleiman yace mutane shida da ake zargin suna taimakawa rundunar da wasu bayanai da zai taimaka wajen kama duk wanda yake da hannu a cikin rikicin.

Rikicin wanda ya yi sanadiyar asarar rayuka da dukiya mai yawa wanda kuma hakan ya sa gwamnatin jihar ta Adamawa ta sanya dokar hana zirga zirga a yankin.

Related posts

Leave a Comment