Abuja: Fusatattun Matasa Sun Yi Zanga-Zanga A Hedikwatar APC

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar wani rikici ya barke a shalkwatar jam’iyyar APC mai mulkin da ke Abuja a ranar Alhamis.

Wasu matasa masu zanga-zanga sun hallara a ofishin jam’iyyar inda rahotanni suka bayyana cewa masu zanga-zangar sun rika yin wakoki suna sukar shugaban jam’iyyar Abdullahi Adamu.

Rahoton ya ce matasan sun fito daga jihar Kogi ne, kuma sun isa shalkwatar ne yayin da jam’iyyar ke wani taro.

Masu zanga-zangar na nuna bacin ransu ne kan abin da suka kira “kwace tikitin takarar mukamin dan majalisar wakilai da aka yi wa gwamninsu” kuma aka mika shi ga wani mutumin na daban.

Jami’an tsaro sun kulle kofofin babban ofishin jam’iyyar yayin da suka ji masu zanga-zangar na ikirarin hana Abdullahi Adamu ficewa daga ginin.

Related posts

Leave a Comment