Sarauniyar Ingila Elizabeth ta II, basarakiyar da ta fi dadewa a kan karagar mulkin Birtaniya, ta rasu a Balmoral tana da shekaru 96.
Sarauniya Elizabeth ll ta hau kan mulki ne a shekarar 1952 kuma ta ga sauye-sauye da dama ta rasu ne bayan ta shafe shekaru 70 akan mulki.
Babban danta Yarima Charles ne zai jagoranci kasar wajen jimami a matsayinsa na sabon Sarki da kuma shugaban kasashe 14 na kungiyar Commonwealth.
A wata sanarwa sabon Sarki ya ce: “Mutuwar mahaifiyata abar kaunata Mai Martaba Sarauniya, lokaci ne na matukar bakin ciki a gare ni da dukkan iyalaina.
“Muna matukar jimamin rasuwar Basarakiya abar bege kuma mahaifiyata abar kaunata. Na sani cewa rashinta zai matukar yi wa ‘yan kasar nan da Commonwealth zafi.”
Ya kara da cewa a yayin da suke jimamin rasuwarta da kuma sauyin da aka samu, shi da iyalansa za su “nutsu da kwanciyar hankali ne bisa sanin cewa duk fadin duniya ana girmamawa da kuma kaunar Sarauniya”.
A sanarwar da Fadar Buckingham ta fitar ta ce: “Sarauniya ta rasu salin-alin a Balmoral da rana.
