Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar ?an takarar shugaban kasa na jam`iyyar APC Bola Ahmed Tinubu, ya gana da Gwamnan Jihar Ribas Nyesom Wike da wasu gwamnonin PDP a shirin da yake yi na samun nasara a babban za?en 2023.
Tawagar Gwamna Wike ta kunshi Gwamnan Oyo Seyi Makinde da na Binuwai, Samuel Ortom da na Abiya, Ikpeazu Okezie.
Alhaji Ibrahim Masari na hannun daman Bola Tinubu ya shaidawa BBC cewa ganawar ta mayar da hankali ne kan za?en 2023.
A cewarsa, suna da kwarin gwiwar saye zuciyar Wike da wa?annan gwamnoni da jawo hankalinsu domin yi wa APC aiki.
Dangane da batun ko Wike zai dawo APC Ibrahim Masari ya bayyana cewa ba lallai sai mutum ya sauya jam’iyya zai iya taimaka wa wani domin nasarar zabe ba.
Alhaji Masari ya kara da cewa “a siyasar zamani ba ka bukatar mutum ya dawo jam’iyyar ka kafin ya taimake ka”.
