Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar a ranar Laraba Kungiyar Izalatul Bidi’a wa Iqamatus Sunnah ?ar?ashin jagorancin Shugaba Imam Abdullahi Bala Lau reshen babban birnin tarayyar Abuja ta gudanar da auren ‘yan mata marayu guda 20.
Kwamitin kungiyar na babban birnin shi ne ya shirya bikin daurin auren a karkashin inuwar kungiyar ta kasa. Bayan daura auren an bai wa ma’auratan kayan daki da jari na tsabar kudi domin yin sana’a.
Wasu daga cikin Amaren da aka zanta dasu sun godewa kungiyar ta Izala bisa ga alheri da ta yi musu tare da addu’ar Allah ya yi wa shugabannita jagoranci.
Kungiyar ta Izala ta yi fice wurin gudanar da ayyukan alheri da bada gudunmawa wajen ciyar da addinin musulunci gaba a tarayyar Najeriya da kasashen ketare.
