Gwamnan Kaduna: Goyon Bayan El Rufa’i Ga Uba Sani Ya Sauya Lissafi

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Sani Dattijo, tsohon Shugaban Ma’aikatan Gwamna Nasiru El-Rufa’i ya sanar da janyewar tsayawa takarar Gwamna a Shekarar 2023, biyo bayan amincewa da Gwamnan yayi ma abokin hamayyar sa Uba Sani.

Sanata Uba Sani wanda yake Wakiltar Kaduna ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, shine ?an Takarar da ma?arraban Gwamnan suka za?a, dana kusa da Gwamna, da Iyalai da kuma ?an Siyasar APC Gidan Gwamnatin Jihar Kaduna

A wani taron gaggawa na masu ruwa da tsaki da Gwamna El-Rufa’i ya kira a ranar Laraba, Gwamnan ya gabatar da bu?atar za?ar ?an takara ta hanyar sasanci, a gaban masu ruwa da tsaki na gidan Gwamna.

Wa?anda suka halarci taron sun ha?a da Mataimakiyar Gwamnan Jihar Hadiza Sabuwa Balarabe, da Sakataren Gwamnatin Jihar Balarabe Abbas Lawal, Shugaban Majalisar Dokoki Yusuf Zailani, da Sanata Mai wakiltar Kaduna ta tsakiya Uba Sani, tsohon shugaban Ma’aikatar Gwamna, Sani Dattijo da sauran masu ruwa da tsaki.

Wata majiya da ta halarci tattaunawar taron ta na?alto Gwamnan yana cewa yaso mai gadon shi da farko itace Mataimakiyar Gwamna Hadiza Balarabe, amma ya jefar da wannan tunanin, bayan ya tattauna da Shugabannin Addinai, dana Siyasa da sauran masu ruwa da tsaki.

Gwamnan ya ?ara da cewa, tunda tikitin Hadiza Balarabe bazai iya tafiya a banza ba, to don haka ya za?i Uba Sani a matsayin ?an Takarar Gwamna daya za?a.

Gwamnan ya kuma yi wani canje-canje, inda ya bukaci Hadiza Balarabe ta cigaba a matsayin Abokiyar Takarar Uba Sani, damar da ta?i amincewa da ita nan take.

Gwamnan ya kuma umarci Sani Dattijo daya canja maza?a ya nemi takarar Sanatan Kaduna ta Tsakiya.

Wa?anda suka halarci taron sun ce Dattijo nan take yayi gaggawar amincewa da hukuncin Gwamnan cikin farin ciki.

A yayin da mu?arraban Gwamnati suka amince da matsayar El-Rufa’i, amma har yanzu, Uba Sani zai je Zaben fidda gwani da sauran ?an Takaran APC da suka ha?a da Manajan Darakta na Hukumar NIMASA Bashir Jamo, da Alhaji Sani Sha’aban Surukin Shugaban Kasa Bahari, da yace shi bai amince da hukuncin kama karya na Gwamna Nasiru El-Rufai ba sai an je an buga a Zaben fidda gwani.

Related posts

Leave a Comment