Harkar kiwon lafiya harka ce da ta rataya awiyan gwamnatocin jihohi dana tarayya dama kananan hukumomi , kamar yadda dokar kundin tsarin mulkin kasa ya tanada. Wakilin muryaryanci.com ya samu damar zantawa da mataimaki na Musamman ga shugaban karamar hukumar Garko dake jahar Kano a inda yayi kira ga Gwamnatin jahar kano da ta daga darajar Asibitin Garko zuwa ga Babban Asibitin kula da marasa lafia wato ‘ General Hospital’
Hon Baban Tatu ya roki Gwamnatin Jahar kano Karkashin jagorancin Khadimul Islama Abdullahi Umar Ganduje da ta duba wannan koke nasu da idon rahama domin anfanar al’umar Jihar Kano baki daya.
Mayar da Asibitin garin Garko ya zuwa babban asibiti da akafi sani da General Hospital zai tamakawa Al’umar yankin dake da Garin Dagatai Goma sha Tara(19) gami da Maza6u Goma , kimanin shekara Goma sha biyar kenan muna wannan kira to Amman lokaci yayi da mu al’umar Garko zamuyi dukkan mai yiwuwa wajen ganin mun ribatu da ribar demokaradiyya , muna kira ga dukkan wakilan mu na majalisu tun daga kan dan majalisar dattawa da yake wakiltan mu , Dan Majalisar taraiya , Dan Majalisar dokoki na jiha da su yiwa Allah Su-mai da hankali akan harkar lafia domin harkar lafia agarin Garko nacikin halin ha’ula’i.
Asibitocin mu da suke kauyuka irinsu Lamire , kafin Malamai , Makadi , Garin Ali , Sarina , zakarawa da Garwaji sun Riga da sun zama , kangon beraye da gafiyu da Karnuka,”kamar yadda Hon Baban Tatu ya shaida mana”
Wannan bakaramin koma baya bane ga Karamar hukumar Garko. Hon. SSA Babantatu ya cigaba da cewa aduk fadin kana-nan hukumomin kano ta kudu sune koma baya ta fannin ababan more rayuwa, wannan yasa suke rokon Mai-girma Gwamna, ‘yan majalisu da dukkan masu ruwa da tsaki na karamar hukumar garko da suyiwa Allah suyi dukkan mai yuwuwa wajen ganin an inganta harkar lafia a wannan yanki nasu.
Hakazalika munji ta bakin Kwararru masu kula da wannan asibiti na Garin Garko ko yaya suke ganin irin wannan kiranye kiranye da ake Yi na daga darajar asibitin garin Garko?
Baffa Nasiru shine babban jami’in dake jagorancin asibitin Kuma ya shaidawa wakilin muryaryanci.com cewar “wannan al’amarine mai muhimmanci musamman idan akai la’akari da dunbin al’umar dake amfana da wannan asibiti kimanin kananan hukumomi hudu da suka hada da, Bunkure , kibiya , Rano da dawakin kudu ne ke amfana da wannan asibiti na Garko a kullum, sannan suna duba marasa lafiya kimanin Dari da Hamsin ya dan-ganta da irin yanayin da akasamu kai musamman adadai wannan lokaci da ake fama da Zazzabin Cizon Sauro (Malaria) ta bangaren haihuwa kuwa ko wanne wata suna kar6ar haihuwa kimanin Dari da Goma zuwa Dari da Ashirin.
Shima babban Sakataren asibitin Mal. Musa S. Kanawa yayi Karin haske kan irin al’umar dake cin gajiyar shi wannan asibiti kamar yadda yake cewa a duk wata suna kar6ar haihuwa kimanin jarirai 120 a tsakanin wadannan kananan hukumomi dake cin gajiyar shi wannan asibiti na Garko .
Daga karshe masu ruwa da tsaki na wannan Kananan hukumomi sunyi kira na musamman ga Maigirma Gwamnan Kano Attajirai da ma dukkan masu fada aji da adubi wannan bukata tasu duba da Muhimmancin lafiya a tsakanin aal’uma domin kuwa komai zakayi sai da lafia.
A bangaren al’uma mazauna wannan yanki da muka zanta dasu suma haka abun yake domin kuwa suna masu ra’ayin lallai lokaci yayi da mahukunta zasu kalli wannan batu domin share musu hawaye.
