Ministan Tsaro, Janar Bashir Salihu Magashi (Mai ritaya), ya bada tabbaci ga iyayen yaran da aka sace a makarantar Kimiyya ta karamar hukumar Kankara, za su dawo nan da awowi kadan, dukkan su za su dawo gidajen su cikin Koshin Lafiya. Saboda mun san inda suke, kuma muna lura da motsin su, abinda muke bukata a cigaba da yi wa jami’an tsaron mu addu’a, domin samun nasara.
Magashi ya bayyana haka ne, a yau lahadi, lokacin da tawagar gwamnatin tarayya, ta zo jihar Katsina, domin jajentawa iyaye da malaman makarantar da gwamnatin jihar Katsina, dangane da sace wadannan dalibai, wanda a halin yanzu akwai sama da dari ukku da talatin da ukku da ke wajen su.
Ministan Tsaron ya kara da cewa ”mun zo jihar Katsina, domin jajantawa iyaye da al’umma jihar Katsina, kan sace wadannan dalibai a Kankara, wanda ba karamin tsaiko ga ilmin su day rayuwarsu. Sakamakon bayanan sirri da muke samu daga jami’an tsaro da ke wannan aiki na kubutar da su, kuma suna samun nasara. Nan da awowi kadan masu zuwa, za mu kubutar da su ba tare da an yi asara ko daya daga cikin Daliban.
Da yake maida jawabi, Gwamnan jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari, ya bayyana cewa zuwa yanzu dalibai dari ukku da talatin da ukku ne ke hannun su ko kuma suka bata. Makarantar na da yawan dalibai dari takwas da talatin da tara, kuma har zuwa yanzu babu wani mutum ko kungiya da ta tuntube mu na ita ke da alhakin daukar wadannan yara ba.
