An gwada a kalla manyan hafsoshin sojin Najeriya masu mukamin janar guda 18 kuma aka gano suna dauke da cutar COVID-19 wadda aka fi sani da suna CORONA.
Ana zargin jami’an sojin sun yi cudanya da marigayi Manjo Janar Olu Irefin, wanda ya mutu sakamakon cutar COVID-19 makon da ya gabata.
Kamar yadda wata majiya ta tabbatar, wadanda aka gano suna dauke da cutar sun je taro shugabannin soji na shekarar 2020 da aka yi a wata cibiya a Abuja.
Baya ga nan, an samu labarin yadda marigayi janar Irefin ya kaiwa abokan aikinsa ziyara kafin su je taron. A don haka, NCDC ta umarci sauran sojojin da suka halarci taron da kuma iyalansu da su kebe kawunansu na mako guda.
Gidan talabijin din Channels ya bayyana yadda aka tabbatar an fesa magungunan da za su kashe kwayoyin cutar a dakin taron a kwanakin karshen mako.
Dama janar Irefin ya fara ciwo ne a makon da ya gabata a wani taron sojoji da suka yi, wanda daga nan aka kai shi asibiti. Daga baya aka gano yana dauke da cutar COVID-19, ana cikin kulawa da lafiyarsa ya mutu.
