Mun Rasa Sojoji Kimanin 500 – Rasha

Ma’aikatar tsaron Rasha ta bayyana al?alumman farko na yawan sojojin da aka kashe a ya?in Ukraine.

Ta ce sojojin Rasha 498 kawai aka kashe, yayin da 1,597 suka samu rauni, kamar yadda kafofin ya?a labaran Rasha suka bayyana.

Adadin ya ci karo da al?alumman da Ukraine ta bayar inda ta ce ta kashe sojojin Rasha 5,840.

Rasha kuma ta yi ikirarin kashe sojojin Ukraine sama da 2,870 kuma kusan 3,700 suka jikkata. Zuwa yanzu Ukraine ba ta bayyana wasu al?alumma ba.

Ba za ta iya tantance i?irarin Rasha ba ko na Ukraine, amma ma’aikatar tsaron Birtaniya ta bayyana cewa sojojin Rasha sun ji jiki.

Tun da farko hukumar agajin gaggawa ta Ukraine ta ce sama da fararen hula 2,000 da jami’ain agaji 10 aka kashe zuwa yanzu.Article share tools

Related posts

Leave a Comment