Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta ce ?arin farashin man fetur da aka samu a ?asar wanda ya kai naira 617 kan lita ?aya rashin tausayi ne da ake nuna wa ?an Najeriya.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, mai ?auke da sa hannun mai magana da yawun jam’iyyar na ?asa Debo Ologunagba, jam’iyyar ta ce bai kamata a rin?a sayar da litar man fetur a farashin da ya zarce naira 150 a Najeriya.
Sanarwar ta zargi gwamnatin Najeriya da gaza warware matsalar tattalin arzi?i da ?asar ke fama da su, tare kuma da ?o?arin tsawwala wa jama’a.
A ranar Talata ne farashin man fetur a Najeriyar ya kai naira 617 a Abuja, da ma wasu sassan ?asar.
Masana harkar man fetur dai sun ta’allaka batun a kan ?arin farashin gangar ?anyen mai a kasuwannin duniya da kuma fa?uwar darajar naira.
A ranar 29 ga watan Mayu ne shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sanar da cire tallafin da gwamnatin ?asar ke bayarwa a ?angaren man fetur.
Lamarin da ya haifar da tashin farashin sufuri da kayan masarufi a fa?in ?asar.
