Za A Kashe Biliyan Uku Wajen Kwaso ‘Yan Najeriya Daga Ukraine – Fadar Shugaban ?asa

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaba Muhammadu Buhari ya amince a kwashi dala miliyan 8.5 domin a kashe su wajen jigilar ‘yan Najeriya a?alla 5,000 da ke Ukraniya.

Wa?anda za a kwaso ?in dai su na ma?ale ne a can sun rasa hanyar dawowa, tun bayan da ya?i ya ?arke tsakanin Rasha da Ukraniya a ranar 21 Ga Fabrairu.

Kamfanin Dillacin Labarai na Najeriya ya ce yawancin ‘yan Najeriya mazauna Ukraniya sun gudu, sun tsallaka cikin ?asar Poland, Romaniya, Hungary da Slovakia.

?aramin Ministan Harkokin ?asashen Waje Zubairu Dada, tare da Ministar Ayyukan Jin?ai da Agaji, ne su ka bayyana haka a Fadar Shugaban ?asa, a ?arshen taron Majalisar Zartaswa da aka gudanar a ranar Laraba.

Mataimakin Shugaban ?asa Yemi Osinbajo ne ya jagoranci taron na ranar Laraba, a Babban ?akin Taron Majalisar Zartaswa da ke Fadar Shugaban ?asa.

Karamin Ministan Harkokin Waje Dada ya ce an sa hannun amincewa a fidda ku?a?en ne bayan da Ma’aikatar Harkokin Waje da Ma’aikatar Ayyukan Jin?ai, Agaji su ka rubuta wasi?ar bai-?aya tare ta abin da za’a kashe wajen dawo da ‘yan Najeriya ?in zuwa gida Najeriya.

Ya ce Kamfanin Zirga-zirgar Jiragen Sama na Air Peace ne aka tuntu?a domin ya samar da jirage uku wa?anda za su ri?a jigila ba dare ba rana, kuma ba ?a??autawa har sai an kwaso su da gaggawa.

Related posts

Leave a Comment