Rahotanni daga Yola babban birnin Jihar Adamawa na bayyana cewar Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ya bayyana jam’iyyar APC a matsayin babban kuskuren Najeriya ta yi a tarihin ta, kuma ya tabbata jam’iyyar ta ci amanar ‘yan Najeriya.
Atiku Abubakar wanda ya bayyana hakan a ranar Asabar 4 ga watan Satumba a garin Yola, jihar Adamawa yayin taro da manyan jiga-jigan APC Wa?anda suka koma PDP, ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da su yi watsi da APC.
Wazirin na Adamawa Ya yi kira ga membobin APC da su barranta da jam’iyyar saboda abin da ya bayyana a matsayin muguwar rawar da ta taka, yana mai cewa sauya sheka daga jam’iyyar ya nuna alamar karshen APC.
“Mun yi babban kuskure a baya ta hanyar shawagi a wata jam’iyyar da ake kira APC. Amma daga yau ina kiran ku mutanen Adamawa da ku bar jam’iyyun ku ku koma PDP domin ita ce fatan talakawan Najeriya.
“Jam’iyyar PDP ce ta raya Jihar Adamawa bayan APC ta kashe ta, ta shigar da jihar cikin halin ci gaban ababen more rayuwa. “Yanzu makarantun mu sun fi kyau kuma cibiyoyin lafiyar mu suna cikin kyakkyawan yanayi. Ina addu’ar wannan taron zai zama farkon watsi da jam’iyyar APC.”
A yayin taron, fitattun tsoffin mambobin APC, ciki har da tsohon sakataren gwamnatin jihar Adamawa, Kobis Thimnu; Cif Daniel Bwala; Lambobin Sali; Umar Bello; Gwamna Ahmadu Fintiri sun tarbi Nedo Geofrey da Philip Gutuwa zuwa jam’iyyar PDP.
