Rahotanni daga Yola babban birnin Jihar Adamawa na bayyana cewar Gwamnatin tarayya ta ce ta kashe akalla bilyan biyu wajen ciyar da daliban makarantun jihar Adamawa kadai karkashin shirin ciyar da dalibai a fadin tarayya.
Ministar tallafi da walwala, Hajiya Sadiya Umar Faoruq, ta bayyana hakan ne a taron bada kayan girki 50,000 ga gwamnatin jihar Adamawa ranar Asabar a birnin Yola.
Sadiya Farouq, wacce ta samu wakilcin Dr. Umar Bindir, jagoran shirin walwala ta kasa, yace shirin ciyar da dalibai na cikin manyan shirye-shirye hudu na ma’aikatar.
Ta yi bayanin cewa gwamnatin tarayya na kashe ?226 million a wata don ciyar da dalibai a jihar Adamawa. Tace kawo yanzu, sama da dalibai milyan 9 aka yiwa rajista kuma sun amfana da wannan shiri a fadin tarayya.
“Na zo nan don wakiltan Shugaban kasa, domin mika kayan girki 50,000 ga gwamnatin jihar Adamawa, don amfani da su wajen ciyar dalibai.” “Kawo yanzu, shirin ya yi rijistan dalibai milyan tara da ake ciyarwa kuma an dauki masu girki sama da 100,000.”
