Rahotanni daga birnin Zazzau dake jihar Kaduna na bayyana cewar Martaba Sarkin Zazzau Malam Ahmed Nuhu Bamalli ya dakatar da hakimai hu?u na Masarautar Zazzau daga mu?amansu.
A wata sanarwa da mai magana da yawun Fadar Zazzau, Abdullahi Aliyu Kwarbai ya fitar jim ka?an bayan sauka daga hawa a yau, an dakatar da hakiman ne bisa sa?a dokokin da aka gindaya na Hawan Sallah.
Hakiman da aka dakatar sun ha?a da Ubangarin Zazzau Alhaji Bashir Shehu Idris da Wakilin Birnin Zazzau Alhaji Suleiman Ibrahim Dabo da Sarkin Dajin Zazzau Alhaji Shehu Umar da kuma Garkuwan Kudun Zazzau Alhaji Muhammadu Sani Uwais.
Ana zargin hakiman da sa?a doka ta uku da ke cikin kundin laifukka da hukunce-hukuncen hawa a Masarautar Zazzau wadda ta haramta wa kowane hakimi yin hawa da ?an tauri ri?e da makamai.
