Shugaban Izala Sheikh Abdullahi Bala Lau, yace aci gaba da yin addu’a Allah ya zaba mana shugaba na gari a wannan zabe dake tafe a tarayyar Naijeriya. “Kungiyar Izalah ba kungiyar siyasa ba ce “inji shi”
Shehin Malamin yace Matsayar kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah wa ikamatis Sunnah wanda muke mata jagoranci shine munsan cewa al’ummar Musulmi guda biyu zuwa uku suna wannan takara al’ummar musulmi suna fatan Allah ya zaba mana mafi alkhairi
Munyi magana kuma mun duba duka munyi nazari munga wanene yafi a ciki munyi magana da shuwagabannin mu na ko ina a matakai na ko ina Don mu isar musu da sakonnin da ya kamata Don ya zamanto samun saukin haddasa gaba da kiyayya ba tare da mun fito kan mumbari munyi wata magana da zai haddasa gaba a tsakanin al’ummar musulmai ba.
Ina fata al’ummar Musulmi zasu ci gaba da addu’a da kiyaye hakkoki na al’ummar Musulmi dukkanin wanda Allah zai shugabantar dashi ya bamu mai tausayinmu, mai kaunarmu wanda zai kawo zaman lafiya, sanadiyyarsa za a samu cigaba da farfadowar tattalin arziki mai yawa.
Sheikh Bala yaci gaba da cewa, idan da lamarin zai canza ya nuna abun zai koma tsakanin wanda Musulmi da wanda ba Musulmi ba, to a lokacin sai muce dole musulmin nan za a yi saboda haka yakamata a gane wannan, kuma muna rokon Allah madaukakin sarki ya mana jagora, yasa a fara zabe lafiya a gama lafiya, ya zaba mana shugaba na gari. Amin.
