Mummunan Hatsarin Mota Ya Ci Ran Wanda Ya Yi Zanen Batanci Ga Annabi

Lars Vilks, mutumin da ya yi zanen batanci ga Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) a kasar Sweden cikin shekarar 2007, ya mutu a wani mummunan hadarin mota a ranar Lahadi.

Tun bayan da ya yi batancin ga Ma‘aiki, ‘yan sanda ne ke biye da shi don kare lafiyarsa.

Hadarin ya faru ne a lokacin da motar da ke dauke da shi ta yi arangama da roka.

‘Yan sanda guda biyu masu kula da shi suma sun rasa rayukansu a hadarin, wanda ya faru a kudancin garin Markaryd.

Wannan mai zane ya mutu, yana da shekaru 75 a duniya.

A watan Yulin wannan shekara, Kurt Westergaard, Baturen kasar Denmark da shi ma ya yi zanen batanci ga Manzo (SAW) ya mutu.

Related posts

Leave a Comment