Lars Vilks, mutumin da ya yi zanen batanci ga Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) a kasar Sweden cikin shekarar 2007, ya mutu a wani mummunan hadarin mota a ranar Lahadi.
Tun bayan da ya yi batancin ga Maaiki, yan sanda ne ke biye da shi don kare lafiyarsa.
Hadarin ya faru ne a lokacin da motar da ke dauke da shi ta yi arangama da roka.
Yan sanda guda biyu masu kula da shi suma sun rasa rayukansu a hadarin, wanda ya faru a kudancin garin Markaryd.
Wannan mai zane ya mutu, yana da shekaru 75 a duniya.
A watan Yulin wannan shekara, Kurt Westergaard, Baturen kasar Denmark da shi ma ya yi zanen batanci ga Manzo (SAW) ya mutu.

