Mufti Menk Ya Jagoranci Nasiha A Walimar Auren Yusuf Buhari

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar a ci gaba da shagalin bikin ?an shugaban ?asa Muhammadu Buhari Yusuf da kuma ‘yar sarkin Bichi Alhaji Nasiru Bayero; Zahra, an yi kasaitacciyar liyafar Luncheon a babban birnin tarayya Abuja.

A ranar juma’ar da ta gabata ne aka daura auren masoyan biyu, inda aka samu halartar masoya daga sassa daban-daban na Najeriya da ma duniya baki daya.

An gudanar da bikin Luncheon wanda ya samu halartar shugaban kasa da sauran manyan Najeriya, ciki har da jiga-jigan siyasa da ake damawa da su a kasar.

Shugaba Buhari ya gayyaci Fitaccen Malamin addinin Islama na Duniya Mufti Menk domin walima ta musamman.

Buhari Sallau, wani mai taimakawa shugaban kasa a fannin yada labarai, ya bayyana wasu daga cikin wadanda suka halarci shagalin a shafinsa na Facebook.

Wa?anda suka ha?a da Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo Shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Bayero Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha Uwar gidan shugaban kasa, uwar ango; Aisha Buhari Uwar gidan mataimakin shugaban kasa, Ladipo Osinbajo Uwar gidan shugaban kasar Nijar Uwar gidan shugaban kasar G/Bissau Matan gwamnoni da sauran manyan baki.

Related posts

Leave a Comment