Gwamnan Filato Ya Roki Fulani Su Yafe Kisan Gillar Da Aka Yi A Jos

Rahotanni daga Jos babban birnin Jihar Filato na bayyana cewar Gwamnan Jihar Simon Lalong ya ro?i Fulanin Jihar Ondo da kuma Gwamnatin Ondo su yafe kisan da wasu ?atagari su ka yi wa matafiya 23 a Rukuba, Jos.

Kisan dai ya faru a ranar 14 Ga Agusta, inda matasan Kiristoci su ka kashe Fulani Musulmai wa?anda ke kan hanyar komawa garin su a Jihar Ondo, bayan sun halarci taron murnar zagayowar shekarar Musulunci a gidan Sheikh ?ahiru Bauchi, a garin Bauchi.

Rahotanni sun tabbatar da an kashe mutum 23, an yi wa 23 raunuka, kuma jami’an tsaro sun ku?utar da fiye da mutum 30.

Gwamna Lalong ya tura ?a??arfar tawaga zuwa Ondo, a ?ar?ashin Mataimakin Gwamnan Filato, Sonny Tyaden zuwa Jihar Ondo domin yin ta’aziyya ga Gwamnatin Ondo da kuma iyalan wa?anda aka kashe wa ‘yan’uwa da iyaye.

Sun kuma tafi da sauran wa?anda aka ku?utar ?in su ka kai su har Jihar Ondo.

A cikin tawagar akwai Mai Martaba Sarkin Wase, Muhammad Haruna, Shugaban Miyetti Allah na Jihar Filato, Nura Mohsmmed da kuma Shugaban Yarabawa mazauna Jihar Filato.

Lalong ya shaida wa Gwamnatin Ondo da Fulanin cewa ba da yawun Gwamnantin Filato ko al’ummar jihar aka kashe Fulanin ba.

Ya ?ara da cewa wasu ?atagari ne, kuma jami’an tsaro sun Kama wadanda ake zargi, za a hukunta su.

Ya ?ara da cewa gwamnatin jihar na bakin ?o?arin ganin irin wannan mummunan lamari bai ?ara faruwa ba.

Gwamna Rotimi Akeredolu ya gode wa Lalong dangane da matakan da ya ?auka, wajen ganin kisan bai fantsama har an ?ara yin asarar wasu rayuka ba.

Akeredolu ya ce lokacin da lamarin ya faru, ya gaggauta hanzartawa kasuwar sayar da shanu, inda ya samu shugabannin Fulanin, ya yi masu ta’aziyya, jimami da alhini.

A jawabin sa, Shugaban ?ungiyar Fulani Mazauna Kudu Maso Yamma, Kabiru Mohammed ya shaida wa tawagar cewa sun yafe, kuma ba za su ?auki fansa ba.

A jawabin sa, ya ce zaman lafiyar wannan ?asa na gaba da komai, don haka ba za su ?ullaci wasu da niyyar yin ramuwar-gayya ba.

Shi da Gwamnatin Ondo sun gode ganin yadda tawagar gwamnatin Filato ta maida sauran matafiyan gidan su a jihar Ondo.

Related posts

Leave a Comment