Barcelona ta ce Lionel Messi ba zai ci gaba da zama a kungiyar ba, sakamakon matsin tattalin arziki.
Messi, mai shekara 34, bai da yarjejeniya da wata kungiya, tun bayan da kwantiraginsa ya kare a Camp Nou a karshen watan Yuni.
Ya amince da sabuwar kunshin kwantiragi da rage albashinsa a kungiyar, sai dai Barcelona ta dogara da idan ta sayar da wasu ‘yan wasan ta biya albashinsa.
Barcelona ta ce Messi ya yi niyar tsawaita kwantiraginsa a Camp Nou da nufin saka hannu ranar Alhamis, amma ta soki hukumar La Liga kan dokar daidaita kashe kudin kungiya da hakan ya yi mata cikas.
?ungiyar ta ce, “Duk da cewa Barcelona da Lionel Messi sun cimma yarjejeniya da kuma amincewa kan ?ulla sabuwar yarjejeniya a yau, hakan ba zai yiwu ba saboda matsalolin ku?i da wasu tsare-tsaren ?ungiyar.
“FC Barcelona tana matu?ar godiya ga ?an wasan sakamakon rawar ganin da ya taka wa ?ungiyar kan gudunmowarsa ga ci gabanta tana kuma yi masa fatan alkheri a rayuwarsa ta ?wallo ta gaba da kuma ta ?ashin kansa,” a cewar ?ungiyar.
