Hukumomi a jihar Kaduna sun ce adadin wadanda suka mutu a cikin wani rikici da ake yi tun daga karshen mako a wasu kauyukan jihar masu makwabtaka da Filato ya kai 27.
Haka ma sun ce an kona gomman gidaje tare da lalata gonakki a cikin rikicin da ya shafi wasu kauyukka hudu na Karamar Hukumar Kauru.
Sai dai a gefe guda kuma sun ce wasu karin dalibai uku na Bethel Baptist High School sun samu kansu daga wadanda suka yi garkuwa da su.
Jihar Kaduna dai na cigaba da fuskantar barazanar ‘yan Bindiga a kusan kullum, lamarin da jama’a ke dangatawa da rashin yin sulhu da Gwamna El Rufa’i ya ki yi da ‘yan Bindiga.
