‘Yan Najeriya Sun La’anci Karin Farashin Mai Da Gwamnatin Tarayya Ta Yi

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa ‘yan Najeriya na cigaa da yin tir da Allah wadai da ?arin farashin litar mai da gwamnatin Tinubu ta yi, wani mazaunin Abuja da ya bayyana sunansa da Abubukar ya shaida wa BBC Hausa cewa a shafin sada zumunta ya ga batun ?ara farashin man fetur zuwa N617 da aka yi wayewar garin Talata a Najeriya.

Ya ce “Gaskiya ana kai talaka bango.

“Yau za ka tashi da wannan, in an jima ka saya. Ba ka san kuma gobe me za ka je ka tarar ba”.

Ya ce kamata ya yi gwamnati ta duba halin da talakawan Najeriya ke ciki.

Ita ma wata mazauniyar Abuja ta ce abin takaici ne yadda aka wayi gari da ?arin ku?in man fetur ba zato ba tsammani.

“Babu wani bayani na cewa za a yi ?arin (ku?in man). Nawa ne albashin mutum da har za a yi ?arin man fetur da tsada haka?” Ta tambaya.

Ta ce da tsakar rana ne kawai ta ga ana maganar ?arin man fetur ?in a shafin Tuwita.

“Kuma ga shi ina bu?atar na sha man a yau. Farashin da na gani ya kai N617, wannan abu ya wuce hankali. Ba mu gama sabawa da wancan ?arin man fetur ba, sai ga wani. Ni, ban san yadda zan yi ba!”

An samu dogayen layukan ababen hawa a gidajen mai cikin wasu sassan Najeriya, bayan rahotannin ?ara farashin man fetur zuwa sama da N600 a kan lita ?aya. Tun farko, an wayi gari ne da ?arin kashi 22% a kan farashin N540 da ake sayar da man fetur ?in a baya.

Wakilinmu ya fahimci cewa layukan ababen hawan sun faru a gidajen man da ba su kai ga ?ara farashinsu ba. Matakin na zuwa ne yayin da hukumar kayyade farashin man fetur ta kasar ta ce an samu raguwar man da ake sha a kasar daga lita miliyan 65 a kullum zuwa lita miliyan 35 a kullum.

Related posts

Leave a Comment