Kano: Sheikh Daurawa Ya Koma Shugabancin Hisbah

FB IMG 1709460172709

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewa Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya amince ya koma kan mu?aminsa a matsayin Kwamandan Hukumar Hisbah domin ci gaba daga inda ya tsaya.

Daurawa ya amince da hakan ne bayan da malamai suka shiga suka suhulta tsakaninsu da Gwamnan Kano, Abba Kabir.

Tun farko, Malam Daura ya sanar da ajiye mu?amin nasa cikin wani faifain bidiyo da aka ya?a inda aka ji shi yana bai wa Gwamna Kabir ha?uri kana daga bisani ya ce ya ajiye shugabancin Hisbah.

Gwamna Kabir ya yi ?orafi kan yadda hukumar ta Hisbah ke gudanar da aikinta inda ya ce jami’an hukumar kan kama matasa maza da mata suna jefawa a bayan mota kamar dabbobi, lamarin da ya ce bai kamata ba.

Sai dai wasu na ra’ayin cewa Gwamna Kabir ya soki aikin Hisbah ne saboda kama fitacciyar ‘yar TikTok ?in nan ta Kano, wato Murja Kunya, wadda ta kasance ?aya daga cikin masoyiyan Abba Kabir.

MANHAJA ta kalato an ga Malam Daurawa bisa rakiyar wasu malamai a Fadar Gwamnatin Kano a lokacin da suka je tattaunawa.

An ce Dr Said Ahmad Dukawa shi ne ya yi magana da ‘yan jaridu a madadin majalisar malaman inda ya ce Malam Daurawa zai koma bakin aiki.

Wa?anda suka halarci zaman sulhun sun ha?a Farfesa Musa Borodo da Farfesa Salisu Shehu da sauransu.

Related posts

Leave a Comment