Matsin Lambar ‘Yan Najeriya Ne Yasa Buhari Yin Takara – Garba Shehu

Labarin dake shigo mana daga Birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin watsa labarai, Garba Shehu, ya ce yan Najeriya ne suka matsawa Shugaba Muhammadu Buhari don ya tsaya takarar shugaban kasa.

Garba Shehu wanda ya bayyana a shirin Channels TV na Sunrise Daily a ranar Juma’a, 7 ga watan Janairu, ya ce shugaban kasar ya yi daidai da ya ce ya yi iyakan kokarinsa na gina Najeriya.

“Shugaban kasar ya kan kasance mutum mai sauki sosai wasu lokutan wajen yin magana da kuma raha; ina ganin wannan shine abun da mutane suka gaza fahimta game da shi. Ya kamata su fahimci yadda aka lallashe shi da kuma matsa masa don ya yi takara a karon farko.

“Ya yi aiki a matsayin gwamna, minista da kuma shugaban kasa a mulkin soja kuma wannan shine matsayi mafi girma da zai iya kaiwa.

Ya yi ritaya ya koma gida sannan yan Najeriya suka zo suka ce kaine mutumin da ya dace a wannan lokaci, muna bukatarka. Sai da aka yi lallashi.

Related posts

Leave a Comment