Wata babbar kotun tarayya mai zamanta a Garki a babban birnin tarayya Abuja ta yi watsi da karar da aka shigar da ke neman a binciki shugaban hukumar zabe ta INEC game da zargin ba da bayanan karya kan kadarorin da ya mallaka.
A hukuncin da aka yanke a ranar Laraba, mai shari’a M.A Hassan ya gano cewa, Mahmud Yakubu na INEC ya bi ka’idojin da ake bukata wajen bayyana kadarorinsa ga hukumar gwamnati.
Mai shari’a Hassan ya kuma bayyana cewa, abubuwan da Mahmud ya mika sun yi daidai da doka, Hukuncin ya kuma bayyana cewa, duba da cewa shugaban na INEC ya bi doka, don haka babu bukatar wani bincike daga hukumomin tsaro kamar yadda mai shigar da kara ya bukata.
Hukuncin da aka yanke yana martani ne ga kara mai lamba FCT/HC/GAR/CV/47/2022 da Somadina Uzoabaka ya shigar, Uzoabaka ya yi zargin cewa, akwai lam’a da kura’kurai a kadarorin da Mahmud ya bayyanawa gwamnati, don haka ya nemi kotu ta ba hukumomin tsaro damar bincikar shugaban.
