Inganta Tsaro Ne Maganin Matsalar Najeriya – Obasanjo


labarin dake shigo mana daga Birnin Ikko na jihar Legas na bayyana cewar Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya ce mayar da hankali da kuma aiki shi ne zai iya mayar da yawan jama’ar kasar nan zuwa masu amfani da amfanarwa.

A yayin jawabi ranar Juma’a a wajen wani taro a Legas, Obasanjo ya nuna damuwarsa kan yadda yawan jama’a ke hauhawa a kasar nan, ballantana matasa marasa aikin yi, wanda hakan ke ?ara jefa ?asar cikin wani mawuyacin hali.

Tsohon shugaban kasan yace ganin yawan rashin aiki yi da kuma gazawar kasar nan wurin lamurran mulki, matasa masu yawa sun fada harkar tada hankula da garkuwa da mutane.

“Tambayoyi na farko su ne: Ta yaya za mu ciyar da mutanen nan? Ta yaya zamu samar musu da muhalli, ta yaya zasu samu ilimi? Matukar akwai tsaro da sauransu ai ba matsala bane,” yace.

“Jerin tambayoyi na biyu su ne: Ta yaya zamu kiyaye yawan zugar matasa marasa aikin yi? Ta yaya za mu hana su shiga kungiyoyin tada hankula da kuma kungiyoyin masu garkuwa da mutane?

“Yawan mutane da ba a iya sarrafa su abun tsoro ne

“Wannan ne ya bayyana a matsayin hanyar shawo kai. Aiki a siyasance zai iya sa yawan mutane ya zama mai amfani, ina ga wannan ita ce mafita.”

Related posts

Leave a Comment