Matsalolin Najeriya Ya Kamata Ku Yi Batu Ba Komawar Mulki Kudu Ba – Matasan Arewa Ga Gwamnonin Kudu

Kungiyar cigaban Matasan Arewacin Najeriya ta yi tir gami da takaicin yadda sakamakon taron ?ungiyar gwamnonin Kudancin Najeriya ya kasance, maimakon su mayar da hankali wajen tattauna batun matsalolin ?asa sai suka ?ige da batun komawar mulki zuwa kudu.

Kungiyar Matasan ta Arewa ta bayyana hakan ne a cikin wata takardar sanarwa da ta fitar wadda ta samu sanya hannun Shugaban ?ungiyar na ?asa Alhaji Gambo Ibrahim Gujungu, kuma aka rarraba ta ga manema labarai a Kaduna.

Matasan sun bayyana cewar a fili yake Najeriya na fuskantar manyan matsaloli da kalubale musanman akan harkar tsaro, to zai zama abin mamaki idan ya zamana taron gwamnonin Kudu ya kammala ba tare da ta?o wannan magana ba sai suka ?are da batun maganar komawar mulki zuwa Kudu.

“Muna shawartar gwamnonin na Kudu da cewar kafin su kai ga batun komawar shugabancin Kudu, kamata ya yi su mayar da hankali akan matsalolin dake addabar Jihohin su da tunanin lalubo hanyar magance su amma ba kawai su bar Jaki su koma dukan taiki ba.

Kowa na sane da halin da Jihohin kudu suke ciki a yanzu, ?angaren Kudu maso yamma ga fitinar Sunday Igboho, hakazalika a bangaren Kudu maso gabas ga fitinar Nnamdi Kanu da kungiyar shi ta IPOB, ya kamata a magance wannan kafin surutun inda shugabanci zai koma.

Related posts

Leave a Comment