Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Mai girma Shugaban ?asa Muhammadu Buhari da mataimakinsa, Yemi Osinbajo, zasu kashe tsabar kudi har N3.2 billion wajen tafiye-tafiye kadai a shekarar 2022 da muke dunfara.
Wannan na kunshe cikin kasafin kudin 2022 da Buhari ya gabatar gaban yan majalisa ranar 8 ga Okotba 2021 domin su duba kuma su amince da shi.
A bayanan kudaden, shugaban kasan zai kashe N2.3billion wajen tafiye-tafiye da sufuri na ofishinsa yayinda shi kuma mataimakinsa aka shirya masa N778.2 million.
Hakazalika fadar shugaban kasar aka kebe mata N162.25 million don sufuri.
Bayani dalla-dalla Ofishin Buhari 1. Tafiye-tafiyen cikin Najeriya – N775.6 million 2. Tafiye-tafiye zuwa kasar waje – N1.53 billion.
Ofishin Osinbajo 1. Tafiye-tafiyen cikin Najeriya – N301.9 million 2. Tafiye-tafiye zuwa kasar waje – N476.2 million.
A shekarun baya, rahotanni sun nuna cewa shugaba Buhari da mataimakinsa sun kashe N1.5 billion a 2019 don tafiye-tafiye da abinci; N1.52 billion a 2018; N1.45 billion a 2017 ; sannan N1.43 billion da 2016.
