Adamawa: An Shawarci ‘Ya’yan APC Su Hada Kai Domin Lashe Zabe

Jam iyar A P C a jahar Adamawa ta bukaci ya yanta da sukasance masu hada Kansu a koda yaushe domin ganin sun samu nasaran lashe Babban zaben shekara ta dubu biyu da ashirin da uku.

Sakataren tsare tsaren jam iyar A P C na riko kuma dan takaran shugaban jam iyar A P C a matakin jahar Ahmed Lawan ne yayi wannan kira a zantawarsa da muryar yancin a yola, fadar gwamnatin jahar Adamawa.

Ahmed Lawan yace hadin kai a tsakanin yan jam iyar yana da muhimmanci mutuka wanda acewarsa hakan ne zai taimaka wajen samun nasara a zaben shakara ta 2023.

Ya kuma shawarci yan jam iyar ta A P C da su kaucewa duk abinda zai kawo rarrabuwan kan yan jam iyar da kuma daina nuna banbanci domin samun cigaban jam iyar dama jahar ta Adamawa baki daya.

Hawayau Ahmed ya nemi da shuwagabanin dama yan jam iyar da sukasance masu adalci a koda yaushe tare da sakewa wakilain zabe mara domin basu damar zaban wanda sukeso, don haka ya kamata a kaucewa dauki dara wanda hakan bazai haifarwa jam iyar da mai idoba.

A acewarsa dai yin adalci ne yasa jam iyar tayi nasaran cin zabe a shekara ta 2015 don haka ya zama wajibi azo a hada kai domin ganin Jam iyar ta A P C ta kai gaci a zaben shekara ta 2023.

Ahmed Lawan ya kuma kirayi al umman jahar Adamawa da su hada kai tare da daina nuna banbancin siyasa da wanda acewarsa hakan zai taimaka wajen cigaban jahar dama kasa baki sarki

Adamawa: Ya kirayi yan Najeriya da su cigaba da yin adu oi domin neman taimakon Allah madaukakin sarki wajen kawo dukkanin kalubalen tsaro a fadin kasan nan baki daya.

Related posts

Leave a Comment