Rahotanni daga birnin Abeokuta na jihar Ogun na bayyana cewar tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ce kalubalen tsaro sun mamaye gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari fiye da zaton mai tunani.
Obasanjo ya bayyana haka ne a lokacin da yake mayar da martani kan harin da aka kai wa jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja da aka tabbatar da mutuwar mutane a kalla mutum 7 tare da batan fasinjoji 21.
Obasanjo ya ce wannan mummunan al’amari ya nuna cewa ‘yan Najeriya ba su da tsaro a ko’ina – a cikin motoci, a jirgin kasa ko kuma a cikin jirgi. Ya ce kasar na cikin wani mawuyacin hali.
Tsohon shugaban kasar ya yi wannan jawabi ne a gidansa da ke dakin karatu na Olusegun Obasanjo da ke Abeokuta, jihar Ogun yayin da ya karbi bakuncin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Dr Ugochukwu Williams da tawagarsa.
Obasanjo ya bayyana damuwarsa kan yadda ‘yan Najeriya ba su da tsaro a kan hanya, a jirgin kasa da kuma a filin jirgin sama, yana mai kira da a hada karfi da karfe da masu ruwa da tsaki don dakile matsalar rashin tsaro a kasar.
Tsohon Shugaban kasar ya bayyana cewa, al’amura sun mamaye gwamnatin da ke ci yanzu, amma ‘yan Najeriya kada su bari lamarin ya mamaye kasar.
Na yi imani ya kamata mu zauna tare mu dubi halin da ake ciki. “Yanayin da ba ka da tsaro a kan hanya, ba ka da tsaro a cikin jirgin kasa, ba ka da tsaro a filin jirgin sama, yana nuna wani yanayi mai tsanani ne. “Na yi imanin cewa duk ‘yan Najeriya masu tunani dole ne su san cewa akwai mummunan yanayin da ya mamaye gwamnatin yanzu, amma bai kamata mu bar wannan lamarin ya mamaye Najeriya ba.”
