Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shiekh Nuru Khalid ya mayar da martani kan dakatar da shi daga limanci da kwamitin masallacin rukunin gidajen ?an majalisu da ke unguwar Apo a Abuja ya yi masa
A hirarsa da BBC malamin ya ce gaskiya ce ya fada a hudubarsa ta Juma’a kuma bai yi nadama ba.
“Idan suka ce na daina fa?in gaskiya a Najeriya, na daina cewa a daina kashe mutane, to gara na yi dako ya fi mun limanci”
Kwamitin Masallacin ?ar?ashin jagorancin Sanata Dansadau ya ce ya dakatar da malamin ne saboda hudubarsa ta tunzura jama’a.
Amma a martaninsa Sheikh Nuru Khalid ya ce ya yi mamakin mutumin da ya fito daga Zamfara, jihar da har yanzu babu zaman lafiya zai fito ya ce ya dakatar da shi saboda ya yi wa’azi kan hana kashe al’umma?
A cewarsa, kashe kashe bai zama tunzura jama’a ba sai don ya ce talaka ya yi hakuri ya zauna lafiya kada ya fito za?e sai an daina kashe rayukan mutane.
“Ace wai wanda ya fito daga Zamfara ne zai fito ya ce ya dakatar da kai, jiharsa yanzu haka kamar yadda wani ya rubuta a Tuwita an yi wa mata fya?e ba adadi kuma har yanzu ba zaman lafiya.”
“Mataimakin shugaban kwamitin Masallacin ?an Neja ne amma ba ya iya zuwa yankinsu,” in ji Sheikh Khalid.
Ya ?ara da cewa: “su suke taya mu fa?a ba, yanzu ne don an yi maganar a kawo tsaro ya zama barazana?”
