Babban mai ba shugaban kasa shawara kan harkar tsaro, Mallam Nuhu Ribadu ya yi i?irarin cewa rashin tsaro ya ragu cikin mako biyu bayan na?a sabbin manyan hafsoshin tsaron kasar.
Ribadu wanda ya yi wannan furuci bayan wata ziyara da hafsoshin tsaron suka kai wa Shugaba Bola Tinubu a fadarsa da ke Abuja, ya ce hakan ya tabbata ne saboda ?wararrun hannu da aka za?a a matsayin masu jagorantar sha’anin tsaron Najeriya.
Ya kara da cewa sun ziyarci shugaban ?asar ne don su nuna godiya da damar da aka ba su, ta bayar da irin tasu gudunmawar wajen ci gaban ?asa, za kuma su yi aiki tukuru waje tabbatar da ingantaccen tsaro a fadin kasar.
Ya ce shugaba Tinubu ya bayar da tabbacin cewa zai ba su cikakken goyon baya domin gudanar da ayyukansu.
Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai babban hafsan tsaro, Manjo Janar Christopher Musa da babban hafsan sojin ?asa, Manjo Janar Taoreed Lagbaja da babban hafsan sojin ruwan Najeriya, Rear Admiral Emmanuel Ogalla da babban hafsan sojin sama, Air Vice Marshal Hassan Abubakar, da kuma mukaddashin babban sufeton ‘yan sanda, Kayode Egbetokun.
