Rundunar ‘yan sandan jihar Taraba ta ce fa?a ya lafa, kuma ba a samu rahoton ci gaba da rikici a wayewar garin ranar Litinin ba.
“Zuwa yanzu kwamshinan ‘yan sandan Taraba CP Yusuf Mamuda Sama’ila yana bibiyar abin da ke faruwa a garin, bayan kafa dokar hana fita, sannan ba a samu sake tashin rikici ba,” in ji mai magana da yawun ‘yan sandan Taraba.
SP Usman Abdullahi Jada ya ce ‘yan sanda sun kama matasan da ake zargi suna da hannu a rikicin. A cewarsa, wasu a ciki sun je kwasar ‘ganima’ ne, sannan an kama wasu da ake zargin da hannu a kashe-kashe, yayin da aka kama wasu bisa zargin cinna wuta a gidaje.
Ya ce wasu ma bincike ya tabbatar da hannunsu a rikicin, har ma an gabatar da su gaban kotu, kuma tuni kotu tana bin kadin ?ararrakin.
A cewarsa, bayan rikicin farko da na biyu a makon da ya wuce, ‘yan sanda sun kama a?alla mutum goma sha biyar zuwa sha shida.
“Amma na Asabar ?in nan, ba wanda aka kama tukunna,” in ji Usman Jada. “Ana ?o?ari a ga mutane sun koma hayyacinsu”.
