Matsalar Tsaro: Da Yiwuwar A Soke Zaben 2023 – INEC

Hukumar Za?e Mai Zaman Kanta a Najeriya ta yi garga?in cewar babban za?en ?asar da ke tafe ka iya gamuwa babban ?alubalen sokewa idan matsalar tsaro ta ci gaba da addabar wasu sassan ?asar.

Shugaban cibiyar bayar da horo ta hukumar za?en Farfesa Abdullahi Abdu Zuru ne ya bayyana garga?in ranar Litinin a lokacin duba kayan aikin horaswa na hukumar a Abuja babban birnin ?asar.

Ya ce ”duka mun sani cewa tsaro a lokacin za?e abu ne mai muhimmanci ga dimokradiyya , domin tabbatar da samun sahihi kuma ingantaccen za?e a ?asa”.

“Dan haka a cikin shirye-shiryen da hukumarmu ke yi game da za?en 2023, dole mu yi iya bakin ?o?arinmu domin tabbatar da cikakken tsaro ga ma’aikatanmu da kayan aikin za?e da kuma hanyoyin da za mu bi wajen ganin komai ya tafi kamar yadda aka tsara”, in ji Farfesa Zuru.

“Amma idan ba a magance matsalar tsaro da ?asar ke fuskanta ba, hakan zai haifar da soke za?en ko kuma ?age shi a maza?u da dama, lamarin da kuma zai shafi bayyana cikakken sakamakon za?en, abin da kuma ka iya haifar da wasu matsaloli da suka shafi kundin tsarin mulki”.

Hukumar za?en ?asar dai ta saka ranar 25 ga watan Fabrairun wannan shekara a matsayin ranar da za ta gudanar da za?en shugaban ?asa a fa?in ?asar.

Related posts

Leave a Comment