Mai ?akin Darakta-Janar na hukumar jami’an tsaro na farin kaya, SSS, Aisha Yusuf Bichi, ta bada umarnin a tsare ?an takarar gwamna na jam’iyyar NNPP a Kano, Abba Kabir Yusuf, inda ta hana shi hawa jirgi da ga Kano zuwa Abuja.
DAILY NIGERIAN ta jiyo cewa dambarwar ta faru ne a kofar shiga ?angaren matafiya masu alfarma na filin jirgin saman Malam Aminu Kano, yayin da ayarin motocin Yusuf, wanda a ka fi sani da Abba Gida-gida, su ka haifar da cinkoso.
Lamarin ya haifar wa da ayarin motar Aisha Bichi tsaiko, yayin da ta ke shiga ?angaren domin tashi zuwa Abuja.
Majiyoyi sun shaida wa DAILY NIGERIAN cewa lamarin ya fusata Aisha Bichi, inda dogaranta su ka ri?a duka kan mai uwa da wabi da ababen hawa saboda “raina Hajiya”.
Shaidun gani da ido sun ce da ?urar ta lafa, sai Abba Gida-gida ya je don ya yi mata ?orafin abinda dogaranta su ka yi, a matsayin ta na ?awar mai ?akin sa, inda ta ri?a yi masa balbalin-bala’i, har ta ke cewa ba za ta bari ya yi gwamna a Kano ba.
Daga nan dai, in ji majiyoyi, sai ga ?arin jami’an tsaron farin kaya sun zo, inda su ka tsare Abba Gida-gida har sai da Aisha Bichi ta shiga jirgi ta tashi zuwa Abuja.
Wasu majiyoyin ma sun ce kafin ta tashi zuwa Abuja, a lokacin da ta ke ta fa?a, Aisha Bichi ta hango wani hadimin Abba Gida-gida, Garba Kilo yana ?aukar ta a waya, inda ta sa dogaran ta su “harbe shi kuma ba abin da za a yi.”
“Ta ci gaba da fa?a, ta kuma rantse cewa Abba Gida-gida ba zai shiga jirgi ?aya da ita ba. Haka dai aka ci gaba da tsare Abba har sai da jirgin ya tashi matar Daraktan,” in ji majiyar.
