Rahotannin dake shigo mana daga zauren Majalisar dokokin Jihar Kaduna na bayyana cewar ‘yan majalisar Dokokin jihar sun tantance Hajiya Umma Yusuf Aboki, a matsayin kwamishiniyar kasafi da tsare tsare yau Talata.
Hajiya Umma, ta gaji tsohon kwamishinan ma’aikatar Muhammad Sani Dattijo, wanda ya ajiye mu?amin nasa don yin takarar Gwamnan jihar ?arkashin inuwar jam’iyyar APC a zabukan 2023 dake tafe.
