Fina-Finai: An Cigaba Da Shari’ar Hadiza Gabon A Kaduna

Labarin dake shigo mana daga jihar Kaduna na bayyana cewa Jarumar Kannywood, Hadiza Aliyu Gabon, ta fa?a wa Kotun shari’ar Musulunci da ke Kaduna cewa rayuwarta na cikin ha?ari.

Idan jama’a za su tuna wani Bala Musa ya kai ?arar Jarumar ne bisa zargin ta ?i aurensa bayan kashe mata ku?i N396,000. A baya Gabon ta musanta cewa bata san mutumin ba.

Da take jawabi a harabar Kotun, wacce ake zargin ta bakin lauyanta, Barista Mubarak Sani Jibril, ya ce duba da halin rashin tsaron ?asar nan, Jarumar na jin tsoro.

A cewarsa, suna shiga damuwa kowace ranar da Kotu zata yi zaman sauraron shari’ar saboda jarumar na fama da tsegumi a wajen Kotu. Lauyan ya ce: “Tsaro na abun dubawa ne, tsaron jarumar yana da amfani haka kowa da ke cikin Kotun nan har wanda ya kawo ?arar.

“Ba mu san wanda ke bibiyar shari’ar a kafafen sada zumunta ba. Nan gaba zaka iya ganin mutane da bindigu sun zo nan sace mutane, wannan shi ne abun da ya dame mu ba wai shari’ar ba.” Lauyan ya ro?i Kotu ta duba tsaron wacce yake wa aiki ta amince a cigaba da shari’ar ba tare da tana halarta ba.

Da yake martani, Lauyan mai ?ara, Barista Naira Murtala, ya yi watsi da uzurin Gabon na rashin zuwanta zaman Kotu, inda ya ce dole wacce ake ?ara ta halarci zama.

Game da tsaron mai ?ara da wanda ake ?ara, Ya ce ba zai yi musu kan bu?atar ba saboda ?asar ba tsaro, amma yana bu?atar yin nazari a kai.

Alkalin Kotun, Mai Shari’a Khadi Rilwanu Kyaudai ya tabbatar musu da cewa Kotu zata duba tsaron kowane ?angare a zama na gaba.

Related posts

Leave a Comment