Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar Gwamna Abdullahi Umar Ganduje yace gwamnonin arewa ba da gaske suke ba wajen ?aukar mataki a kan kwararar almajirai a jihohinsu, domin an bar abubuwa kara zube kawai a kowace rana Almajirai na ambaliya a Jihohin Arewa.
Yace rashin ha?in kai da aiki tare tsakanin gwamnatocin jihohi shike maida hannun agogo baya a ?o?arin da ake na da?ile kwararar yara almajirai.
Gwamnan ya fa?i haka ne a wani taron manema labarai da ya gudanar kwanan nan a jihar Kano. Ganduje yace: “Almajiranci babbar matsala ce, abunda muke jira shine matakin da gwamnatocin jihohi ya kamata su ?auka na hana kwararan almajirai daga wannan jihar zuwa wata.”
Haka kuma Ganduje yace rashin aiki tare da kuma ha?in kai tsakanin gwamnonin arewa, shine yake da?ile ?o?arin da ake yi na maida almajiran zuwa gidajen iyayen su. Yace: “Kasancewar Kano cibiyar kasuwanci, hakan yasa tana da almajirai daga kowace jiha dake arewa da kuma wasu kasashe kamar Nijar da Chadi.”
“Wasu lokutan idan aka maida almajirai zuwa asalin garuruwan su, sai su riga jami’an gwamnati dawowa, saboda jihar da aka maida su ba su ?auki matakin da ya dace ba.”
