Kungiyar ‘Yan Jarida Ta Yi Watsi Da Umarnin NBC Na Yada Labaran ‘Yan Ta’adda

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Kungiyar Mammalaka gidajen jarida na Talabijin da rediyo a Najeriya sun yi watsi da umurnin gwamnatin tarayya na cewa kafofin yada labarai su daina bayar da bayani kan hare-haren yan bindiga da masu garkuwa da mutane.

Shugaban kungiyar Editocin Najeriya NGE, Mustapha Isah; shugaban gamayyar yan jaridan Najeriya, Chris Isiguzo; da Diraktan kungiyar dokokin kafafen yada labarai, Richard Akinnola, sun yi ittifakin cewa ba zasu bi wannan umurnin.

A cewarsu, ba kafofin yada labarai ke kirkiran labarai ba, kawai suna sanar da mutane abinda ke faruwa ne.

Sun shawarci gwamnatin Buhari ta magance matsalar tsaro maimaikon yunkurin toshewa yan jarida baki da suke han?oron yi.

“NBC ta ce kafafen watsa labarai su daina kawata hare-hare kuma na yarda da hakan, amma ina da matsala da maganan cewa a daina bada rahotanni. Ban san abinda suke nufi da hakan ba.

“Kafafen watsa labarai ba su ke kirkiran labarai ba. Idan akwai harin yan ta’adda, zamu ruwaito. Ba zamu daina aikinmu ba duk da barazana.”

Shima shugaban NUJ, Isiguzo, yace ba za su bari gwamnati ta toshewa kafafen yada labarai baki ba ta kowani hali.

“Wajibi ne hukumar ta sake duba wannan umurni. NBC ta tabbatar da cewa abubuwan da take yi na muwafaqa da abubuwan dake faruwa a kasashen duniya.”

Akinola kuma yace wannan umurni wani hanya ne na kokarin kwacewa yan Najeriya muryarsu.

“Gwamnati ta gaza wajen bayar da tsaro kuma wannan hakkinmu ne mu bayyanawa duniya inda gwamnati ta gaza.”

Related posts

Leave a Comment