Matasan APC Sun Goyi Bayan Shugabanci Ya Koma Kudu

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Matasan jam’iyyar APC a arewa sun nuna goyon bayansu ga kiran da ake yin a jam’iyyar ta mika tikitinta na shugaban kasa ga yankin kudu.

Matasan, karkashin kungiyar ‘Concerned Northern APC Youth Forum’, sun ce bayan tuntubar da suka yi a fadin jihohin arewa 19, sun yanke shawarar cewa jam’iyyar ta mika kujararta na shugaban kasa ga yankin Kudancin kasar.

Yayin da yake jawabi ga manema labarai a ranar Talata, 22 ga watan Fabrairu, shugaban kungiyar, Suleiman Liba, ya ce ya zama dole a nuna adalci da daidaito wajen zabar shugaban kasa na gaba a shekarar 2023.

Related posts

Leave a Comment