Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar wata Babbar Kotun Tarayya ta ba wa hukumar ya?i da miyagun ?wayoyi NDLEA damar ci gaba da tsare ?an sanda DCP Abba Kyari bayan ta kama shi kan zargin safarar hodar ibilis wato koken.
Mai Shari’a Zainab Dimka Abubakar ce ta ba da umarnin bayan wata bu?ata da hukumar ta shigar da zimmar neman ci gaba da tsare DCP Kyari da wasu mutum shida tsawon mako biyu.
Wa?anda za a ci gaba da tsarewar su ne: DCP Abba Kyari, ACP Sunday J. Ubia, ASP James Bawa, Sufeto Simon Agirigba, Sufeto John Nuhu; Chibunna Patrick Umeibe, Emeka Alfonsus Ezenwanne.
Sanarwar da NDLEA ta fitar a ranar Talata ta ce wanda ake zargi da safarar koken ?in na 6 da na 7 (Umeibe da Ezenwanne) sun amsa laifinsu cewa sun shigar da ita Najeriya ne daga Ethiopia.
Ta ?ara da cewa su kuma wa?anda ake zargi na 1 zuwa na 5 ((Kyari, Ubia, Bawa, Agirigba, Nuhu) ‘yan sanda ne da suka kama na 6 da na 7 kuma suka kai su NDLEA don yin bincike.
“Saboda binciken da NDLEA ta gudanar ya nuna cewa na 1 zuwa na 5 sun ci amanar aiki kuma sun shiga an dama da su wajen safarar miyagun ?wayoyi da kuma saka hannu wajen lalata hujja a kan masu laifi ta mua’amala da koken,” a cewar sanarwar.
