Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Matasan jamiyyar APC a arewa sun nuna goyon bayansu ga kiran da ake yin a jamiyyar ta mika tikitinta na shugaban kasa ga yankin kudu.
Matasan, karkashin kungiyar Concerned Northern APC Youth Forum, sun ce bayan tuntubar da suka yi a fadin jihohin arewa 19, sun yanke shawarar cewa jamiyyar ta mika kujararta na shugaban kasa ga yankin Kudancin kasar.
Yayin da yake jawabi ga manema labarai a ranar Talata, 22 ga watan Fabrairu, shugaban kungiyar, Suleiman Liba, ya ce ya zama dole a nuna adalci da daidaito wajen zabar shugaban kasa na gaba a shekarar 2023.

