Akwai Babban Kalubale A Zaben Najeriya Dake Tafe – Majalisar Dinkin Duniya

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar a yayin da ake kusa da fara babban za?en 2023 a Najeriya, ofishin majalisar ?inkin duniya na Najeriya ya lissafo wasu damuwowi da yake da su a kan za?en.

Za a gudanar da za?en shugaban ?asa da na ?an majalisar tarayya a ranar 25 ga watan Fabrairu, yayin da za a gudanar da za?en gwamnoni da na ?an majalisar jiha a ranar 11 ga watan Maris.

Babban jami’in Majalisar a Najeriya, Matthias Schmale, shine ya zayyano fargabar da hukumar ke da ita akan za?en a yayin wata tattaunawa da manema labarai

“Muna fargabar a ?aga za?uka saboda rikici,” A cewar sa ba kawai rikicin da ake fama da shi a Arewa maso Gabas ka?ai Mr Schmale, yayi nuni da shi ba, hada rikicin da ake fama da shi a Kudu maso Gabas da wani yanki na Arewa maso Yamma.

Yace rikice-rikicen za su iya shafar gudanar da za?en da kuma sakamakon sa.

Wasu abubuwa guda biyu da Majalisar ke nuna damuwar ta akai sune matsalar rashin man fetur da kuma ?arancin ku?i da ya addabi ko ina a Najeriya.

“Na bayyana ?alu?alen da za a fuskanta a wajen shirya za?en nan lokacin ?auko kayan aiki da ma’aikata zuwa rumfunan za?e, hakan yana da ala?a da rashin man fetur da kuma ?arancin ku?in da ake fama da su,”.

Yace jam’iyyu, ?an siyasa da magoya bayan su, sun yi kalamai na tsana wa?anda kwata-kwata ba su dace ba. Yayi kira da a ri?a tausasa harshe sannan a gudanar da ya?in neman za?e cikin zaman lafiya da mutunta abokan adawa.

Related posts

Leave a Comment