Masu Tallar Nono Na Safarar Muggan Kwayoyi Ga ‘Yan Bindiga – Tambuwal

Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya yi zargin cewa matan da ke tallar fura da nono na safarar mugga kwayoyi da sauran kayan bukatun yau da kullum ga ‘yan ta’addan dake cikin daji, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Gwamna Tambuwal ya yi wannan zargin ne a lokacin da ya karbi tawagar shehin malami Dr Ahmad Gummi a Sokoto.

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal yace ya kamata mutane su saka lura ga wadanda ke kai kawo cikin gari zuwa daji domin a hana bazuwar makamai da ke tunzura ayyukan ta’addanci musamman a yankin mu na arewa.

Gwamnan ya jaddada cewa addinin musulunci, addini ne na zaman lafiya kuma a koda yaushe yana koyar da zaman lafiya da kaunar juna dan haka bai kamata a bar wasu tsirarun mutane su batawa addinin suna ba.

Related posts

Leave a Comment