Labarin dake shigo mana daga jihar Kaduna na bayyana cewar ?an takarar shugabancin ?asa a karkashin jam’iyya mai mulki ta APC Bola Ahmed Tinubu ya ziyarci Birnin-Gwari kafin fara yakin neman zabensa a Kaduna.
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu da tawagarsa sun isa jihar Kaduna inda za su gudanar da yakin neman zabensa a jihar ta Kaduna a ranar Talata.
Tinubun ya samu rakiyar abokin takararsa Sanata Kashim Shettima da babban daraktan yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC kuma gwamnan jihar Filato, Simon Lalong da gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, da na Kebbi, Atiku Bagudu sai kuma na Jigawa, Abubakar Badaru.
Gwamna Nasir El-Rufai da dan takarar gwamna na jam’iyyar APC na jihar, Sanata Uba Sani da wasu manyan jami’an gwamnatin jihar Kaduna ne suka tarbe su a filin jirgin sama dake Kaduna.
Bayan isowarsa jihar ta Kaduna, tsohon gwamnan na jihar Legas ya zarce jaje zuwa karamar hukumar Birnin Gwari, daya daga cikin kananan hukumomin da ‘yan tada kayar baya da ‘yan fashin daji suka addaba don ya gane wa idanunsa halin da yankin yake ciki.
