Ka Yi Gaggawar ?aukar Mataki Kafin Fulani Su Haifar Da Yakin Basasa – Soyinka

Farfesa Wole Soyinka ya jawo hankalin shugaban kasa, Muhammadu Buhari da cewa ya fito yayi magana saboda kada Fulani Makiyaya su haddasa wani yakin Basasa a tarayyar Najeriya.

Soyinka ya bayyana hakane a ganawarsa da BBC Pidgin inda yace idan aka jira sai gwamnati ta dauki mataki akan lamarin to zasu zama bayi a kasarsu wanda watakila ma hakan ya fara faruwa.

Ya kuma bayyana cewa, shi kanshi Fulani Makiyaya sun kaiwa gidansa Hari, amma cikin yardar Allah ya samu nasara daga ku?uta daga harin.

Jama’a na cigaba da bayyana ra’ayoyin su akan halin rashin tsaro da kasar ke fuskanta, wanda ake danganta shi da Fulani makiyaya.

Da dama daga cikin jama’a na ganin da akwai sakacin Gwamnati wajen da?ile ?aruwar fitinar, yayin da wasu ke kallon abin a matsayin wata ajanda ce ta kokarin korar Mutane daga garuruwan su da maye gurbinsu da Fulani.

A kwanan nan babban Malamin addinin Musulunci a kasar Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya samu ganawa da wasu daga cikin ‘yan bindigar, inda ya fito ya bayyana cewar ri?akkun ‘yan ta’adda ne da ya kamata gwamnati ta yi zaman sulhu da su domin kawo karshen fitinar dake faruwa a ?asar.

Related posts

Leave a Comment